Labarai
Kotun daukaka kara ta Sanya ranar sauraron karar Abba da Gawuna
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta sanya ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023, domin sauraren karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar ya na kalubalantar soke zabensa da kotun sauraron kararrakin zabe ta Kano ta yi.
Sanarwar ta nuna cewa za a saurari karar mai lamaba CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a ranar da aka ambata a sama.
Wadanda su ke cikin karar sun hada da Gwamna Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP da jam’iyyar adawa ta APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 20 ga watan Satumba, 2023, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta soke zaben Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana cewa kuri’u 165,663 daga cikin wadanda aka kada masa ba su da inganci, inda ta ce INEC ba ta sanya hannu ko sitamfi a jikinsu ba.
INEC ta bayyana Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023 bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 daga cikin kuri’u 165,663, hakan tasa kuri’un Abba suka koma 853, 939, Gawuna Kuma da ya Sami kuri’u 890,705 ya haura Abban da kuri’u 30,000 .
Sakamakon haka, kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna tare da umurci hukumar zabe ta INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta baiwa Abba Kabir tare da baiwa Gawuna sabuwar shaidar cin zaben.
Sai dai Abba kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP da kuma INEC sun daukaka kara kan hukuncin kotun.
You must be logged in to post a comment Login