Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yakin Isra’el da Hamas: Palastsinawa sun nemi goyon bayan Jihar Kano

Published

on

Gwamnati da al’ummar kasar Falasdin sun bukaci al’ummar musulmin duniya da su ci gaba da taya kasar da addu’oin fita daga cikin mawuyacin halin da suke ciki sakamakon yakin da suke yi da yahudawan Isra’ela.

Jakadan kasar a Nigeria Abdullah Bin shawesh ne ya bukaci hakan lokacin da ya kai wata ziyara jihar kano, Inda ya halarci taron da’awa da kungiyar mata Musulmi ta AMWA ta shirya  masallacin Afdul waham kulafa’urashidin dake unguwar sharada kwanar ganduje.

Bin Shawesh ya Kuma yi amfani da damar wajen tunatar da mahalarta taron kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu, wanda hakan yasa ya nemi dukkanin Musulmin Nigeria su rika Sanya kasarsa cikin addu’o’in su don magance kashe-kashen rayukan al’umma da ake yi kowacce ranar a kasar Falasdin.

Da take nata jawabin shugabar mata musulmai ta africa wato Amwa, Hajiya Aisha Ishak sulaiman ta bayyana takaicin ta kan mawuyacin halin da al’ummar Falasɗinawa ke cini Inda ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addaci da Isra’ila take cigaba da kaiwa Falasɗinawa.

“Zamu saku yan uwanmu a cikin Addu’oi don samun sauki domin muna takaicin irin cinzarafin da akewa yan uwanmu mata a wannan yakin da ake yi na ta’addanci, kuma zamu cigaba da kara dacewa sunanan suna kakari wajan dada fadakar da al’umma akan batun domin kuwa akwai wadanda suke yiwa abin wani irin kallo”.

A nata bangaran Sa’anatu Ali kurawa jagora atafiyar da’awa a nan ‘kano tace sun lashi takobin wayar dakai ga Jama’a ako ina a cikin kasar nan, Inda tace abun da ake yiwa Falasɗinawa bakaramin zalumci bane ga musulmai’.

 

Daga karshe ta yi kira ga kafafen yada labarai da su zama masu yadda labarin gaskiya a kowane lokaci duba da yadda wasu kafafen suke yada labaran shamcin gizo akan yakin.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!