Labarai
Kotun daukaka kara ta soke zaben Alhassan Doguwa
Kotun daukaka kara dake zama a jihar Kaduna soke zaben dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tudunwada da Doguwa a majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa.
Kotun daukaka karar ta rushe zaben da aka yi a kananan hukumomin Tudunwada da Dogawa tana mai tabbatar da cewa an tafka kurakurai a mazabon.
A yayin yanke hukuncin wanda mai shari’a Oludotun Adefope-Okojie, kotun y ace bai dace a gudanar da zaben bayan da aka cire sunayen ‘yan takarar jam’iyyu daga sakamakon zaben.
BATUTUWA MASU ALAKA:
Lauyoyi sun koka kan rashin kotun daukaka kara a Kano
Kotu ta yanke hukuncin kisan kai ga wani matashi a nan kano
Rahotanin sun bayyana cewar, sauran alkalan kotun da suka yanke hukuncin sun hada da Mai shari’a Hussani Muktar da Mai shari’a Sa’id Tanko Husaini.
Wadanda suka shigar da karar sun hada jam’iyyar PDP da dan takararta Air Commodore Salisu Yusha’u
Masu shigar karar sun ce hukumar zabe ta tafka kuskure wajen sanya jam’iyyu biyu a cikin jerin sunayen jam’iyyu 53 da suka shiga zaben.