Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin shugaban Kasar Nijeriya

Published

on

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa a zaɓen 2023.

 

Mai Shari’a John Okoro ya bayyana cewa alkalan kotun sun yi ittifaki wajen tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararraikin zabe ta yanke na tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu.

 

Kotun ta kuma bayyana cewa samun kaso 25 na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya ba sharadi ba ne na lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.

 

“Atiku da Obi sun gaza kawo alkaluman zaben da suka ci karo da wanda INEC ta gabatar.

 

“Saboda haka, sakamakon da INEC ta gabatar shi ne sahihi kuma Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya,” kamar yadda ya sanar.

 

Kotun ta kuma yi watsi da karar da Atiku ya shigar da INEC kan matsalar da shafin tattara sakamakon zaben (iREV) ya samu a lokacin zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

 

Ya kuma bayyana cewa matsalar da shafin ya samu, ba hujja ba ce da za ta sa a soke zabe.

 

A cikin hukuncin da kotun ta karanta cikin minti biyar ta yi watsi da daukaka karar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na LP suka yi zuwa gabanta.

 

Alkalan sun kuma yi watsi da karar da aka shigar na takara biyu a lokaci guda da ake wa mataimakin Tinubu, Kashim Shettima.

 

Kotun ta kuma bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna Tinubu ya yi amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!