Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar sun shigar da kara a kotu

Published

on

Jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sun garzaya kotun sauraron kararrakin zabe domin kalubalantar bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Faburairun da ya gabata.

A jiya Talata ne Atiku Abubakar da Jam’iyyar ta PDP suka shigar da kunshin karar, a kan hukumar INEC da Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jam’iyyar Labour da dan takarar ta Peter Obi su ma suka shigar da karar su ga kotun sauraron karrakin zabe da ke Abuja, inda suke kalubalantar ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!