Labarai
Kotun Malesiya ta daure tsohon firaministan Najib Razak shekaru 15

Kotun kasar Malesiya ta daure tsohon firaministan kasar Najib Razak na tsawon shekaru 15 sakamakon sabuwar tuhumar da ta same shi da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa na wani asusun na musamman da ake zuba kudi,
Wata kotu a kasar Malesiya ta samu tsohon Firaministan kasar Najib Razak da laifin amfani da mukuminsa ta hanyar da ta saba doka, inda ya yi wacaka da dukiyar kasa da aka ajiye a wani asusu na musamman.
Tsohon firaministan Razak wanda yanzu haka yake daure bisa hukuncin dauri. A sabon hukuncin an yanke masa daurin shekaru 15.
Tun shekara ta 2018 lokacin da tsohon Firaminista Najib Razak ya fadi a zaben kasar ta Malesiya, ya ke fuskantar tuhume-tuhume kan zargin cin hanci da rashawa da aka aikata lokacin da yake rike da madafun ikon kasar.
You must be logged in to post a comment Login