Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kuɗin da Ganduje zai kashe a gyaran titin Ahmadu Bello ya yi yawa – SEDSAC

Published

on

Ƙungiyoyin al’umma a Kano sun fara martani kan kashe sama da biliyan guda a gyaran titin Ahmadu Bello.

Gwamnatin Kano dai ta ce aikin gyaran titin zai lashe kuɗi har sama da biliyan guda.

Mai taimakawa gwamnan Kano kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

To sai dai tuni ƙungiyoyin al’umma suka fara martani a kai.

 

Yadda aikin gyaran titin na Ahmadu Bello ke gudana.

Kwamared Hamisu Umar Ƙofar Na’isa shi ne shugaban ƙungiyar bunƙasa ilimi da ci gaban dimukuraɗiyya ta SEDSAC.

Ya ce, kuɗin da aikin zai lashe ya yi yawa, kuma ba shi ne abin da al’ummar Kano suka fi buƙata ba a yanzu.

“Idan aka duba titin a yanzu bai kai lalacewar da za a yi masa wannan gyaran ba, idan ka kalli sauran titunan da ke cikin gari”.

Ya ƙara da cewa, akwai tituna da dama da suka fi wannan lalacewa waɗanda suka fi shi buƙatar gyara, amma ba a mayar da hankali a kansu ba.

“Ga titin Yahya Gusau, titin Hauren Wanki duk gwamnatin Kano ta yi watsi da su”.

Yadda aikin gyaran titin na Ahmadu Bello ke gudana.

Ya ci gaba da cewa, kuma za a iya gyara su da kuɗin gyaran titin Ahmadu Bello.

A ƙarshe ya ce, ya kamata gwamnatin ta riƙa sara tana duban bakin gatari don kada ta riƙa sanya wa mutane shakku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!