Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ku kara hazaka wajen kakkabe ‘yan ta’adda daga Najeriya – Buhari ga jami’an tsaro

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an tsaron kasar nan da su kara kokari wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

 

Shugaban kasar ya kuma yi allawadai da kisan gillar da ‘yan bindiga su ka yi ga wasu jama’a a jihar Zamfara, yana mai cewa gwamnatinsa tana iya kokarinta wajen ganin ta kawo karshen zubar da jinin al’umma a fadin kasar nan baki daya.

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ta ce, zubar da jinin al’umma musamman a wannan lokaci na azumi rashin imani ne kuma abin tir.

 

Ya kuma sha alwshin cewa jami’an tsaro za su zakulo wadanda ke da hannu wajen zubar da jinin jama’a don girbar abin da suka shuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!