Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Za ayi jana’izar tsohon shugaban kasar Chadi Idris Deby a yau juma’a

Published

on

A yau juma’a ake sa ran za ayi jana’izar tsohon shugaban kasar Chadi marigayi Idriss Deby wanda ake zargin ‘yan bindiga sun kashe shi a baya-bayan nan.

 

Rahotanni sun ce shugaba Emmanuel Macron na Faransa da shugaban kula da harkokin ketare na kungiyar tarayyar turai, Josep Borrell suna daga cikin shugabannin duniya da za su halarci wajen jana’izar.

 

Bayanai sun ce janai’zar za ayi ta ne a dandalin La Place de la Nation da ke birnin Ndjamena.

 

A ranar talata da ta gabata ne sojojin kasar ta Chadi suka sanar da rasuwar shugaba Idriss Deby wanda suka ce ya rasa ransa ne sakamakon wani gumurzu da ‘yan tawaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!