Labarai
Kudirin dokar neman rushe hukumar NYSC ya tsallake karatu na farko
Kudirin dokar neman rushe hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar wakilai a yau Litinin.
Dan majalisa Awali Inombek Abiante shine ya dauki nauyin kudirin wanda ya bayyana dalilai da dama da ya ce ya kamata a rushe hukumar ta NYSC.
Kudirin dokar na neman gyara sashe na dari uku da goma sha biyar, biyar cikin baka A cikin baka na kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.
A cewar sa, ci gaba da kashe-kashen ‘yan hidimar kasa a sassa daban-daban na kasar nan da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke yi, ba ya ga rikicin kabilanci da na addini, shi ya sanya ya ga dacewar rushe aikin na hidimar kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login