Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin babban hafsan sojin kasar nan kalubale ne ga matsalar tsaro ― Buhari

Published

on

Sugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mutuwar babban hafsan sojin kasar nan Lutanan Janar Ibrahim Attahiru ya kara ta’azzara kalubalen tsaro da Najeriya ke fama dashi a yanzu.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da tawagar kungiyar gwamnonin da ta kai masa ziyarar ta’aziyyar mutuwar babban hafsan sojin a fadar Asorok.

Ya kuma nuna takaicin sa kan yadda mummunan lamarin kifewar jirgin saman ya afku a lokacin da kasar nan ke fama da kalubalen tsaro.

Haka zalika shugaba Buhari ya tattauna shugaban kungiyar gwamnoni ta kasa kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da takwaransa na jihar Niger, Sani Bello.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!