Labarai
Alarammomin tsangaya sun koka kan rashin ganin Malaman da gwamnatin Kano ta aika musu

Kungiyar Alarammomin tsangaya sun koka kan rashin ganin Malaman da gwamnatin Kano ta tura makarantun tsangaya dan koyar da Almajirai ilimin Zamani.
A cewar Malaman tsangayar malaman da aka turo sun daina zuwa makarantun ba tare da sanar dasu dalilin yin hakan ba.
Tsarin wanda gwamnatin ta dauki malaman sakai 600 tare da biyan su alawus dan koyawa yara almajrai ilimin lissafi da turanci a wasu makarantu fiye da 300 a kanan hukumi 44 na jihar Kano.
Sai dai Malaman tsangayar sunce tun bayan fara wannan shiri malaman da gwamnatin ta tura suka dai na zuwa mafi yawan makarantun da aka tura su.
Alaramma malam Yusuf Wanda aka fi sani da malam babba guda ne daga cikin malaman tsangaya a nan Kano ya ce daliban nasa sun fara gane darasin da aka fara koya musu kwatsam sai malamin ya daina zuwa.
A shekarar 2019 ne gwamnatin Kano ta bullo da shirin shigar da Almajirai na Tsangaya tsarin Karatun , mai taken integrated system of almajiri education a wani mataki na inganta tsarin harkar makarantun tsangaya.
You must be logged in to post a comment Login