Connect with us

Labarai

Ganduje ya kaddamar da shirin makarantun Tsangayu da Al-qur’anai

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da shirin inganta makarantun Islamiyya da na Alqur’ani a nan Kano.

Abdullahi Umar Ganduje ya ce shirin na daya daga cikin goyan bayan da gwamnatin sa ke bayar wa wajen shirin bada ilimi kyauta kuma tilast ga makarantun Firamare da na sakandire, da zummar rage yawan yaran da ba sa zuwa maranta a sassan jihar Kano.

A cewar Gwamnan na Kano ya godewa Allah da ya nuna masa wannan ranar na kaddamar da shirin tallafawa makarantun Isalamiyya wajen bada gudunmawar kayayyakin abinci da kudade ga Alaranmomi da malamai dubu guda daga da Tsangayu dubu guda da suka fito daga kananan hukumomi Arba’in da hudu 44 na jihar nan.

Kazalika gwamnan ya yaba da kokarin da kungiyoyin suke na tallafawa jihar nan da suka hada da DFID da babban bankin duniya da kuma UNICEF.

Gwamnan Abdullahi Umar ya yabawa UNICEF saboda tallafin Naira miliyan dari da biyar 105 da suka bayar ga makarantun Alqur’ani a sassan jihar nan.

Hukuncin Kisa ne ga masu Satar mutane-Ganduje

Malaman Boko zasu fara koyarwa a makarantun Tsangaya-Kano

Mahukunta sun rufe makarantar KCC Kano

Ganduje ya ce gwamnatin sa ta inganta makarantun Tsangayu ne don sanya ilimin boko a ciki kasancewar akwai malaman da za su dinga karantar da darusan Turanci da lissafi a karantun su.

Har’ila yau gwamnan na Kano yayi alkawarin daukar nauyin malaman Alqur’ani don karu ilimin su a kasashe irin su Saudi Arabia don baiwa dalibai ilimin da ya dace.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,404 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!