Labarai
Kungiyar askarawan jihar Zamfara sun halaka wani kasurgumin ɗan bindiga Kacalla Isuhu Buzu

Kungiyar askarawan jihar Zamfara sun samu nasarar halaka wani kasurgumin ɗan bindiga, mai suna Kacalla Isuhu Buzu, a garin Kaya da ke karamar hukumar Maradun.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe dan bindigar ne a yayin wani samame na tsaro, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci da fashi da makami a yankin.
Hukumomin tsaro sun jaddada kudirin su na ci gaba da karfafa yaki da ’yan bindiga, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
You must be logged in to post a comment Login