Kiwon Lafiya
Kungiyar CAJA ta bukaci da a rushe hukumomin zaben jihohi
Daraktan cibiyar wayar da kan al’umma game da shugabanci nagari da kuma tabbatar da adalci CAJA, Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata, ya shawarci masu ruwa da tsaki kan harkar zaben kasar nan su rushe dukkanin hukumomin zaben Jihohi tare da mayar da lamuran zaben kacokan ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
Kwamared Kabiru Sai’du Dakata, ya bayyana hakan ne a jiya ta cikin shirin ‘Mu leka Mu Gano’ na musamman na nan Freedom Rediyo, wanda ya maida hankali kan yadda zaben kananan hukumomin kano 44 da aka gudanar a karshen mako ya wakana.
Kabiru Sai’du Dakata, ya ce, la’akari da yadda zaben ya gudana cike da kura-kurai tare da yadda aka rika yada hotunan da ke nuna yadda al’amuran baki-daya suka kasance, alamu ne na cewa an tabfa magudi a cikinsa.
Haka zalika ya kara da cewa, ba komai aka yi a cikin zaben ba illa barnatar da Dukiyar al’ummar Jihar Kano har kusan Naira Biliyan guda.
Kwamared Kabiru Sai’du Dakata, ya kuma bukaci al’ummar kasar nan da kada su cire tsammanin rashin samun adalci a zabuka masu zuwa sakamakon ganin yadda wannan zabe ya gudana.
Ya kuma ce cibiyarsa ta CAJA ba za ta taba gajiyawa ba wajen ci gaba da wayar da kan al’ummar kasar nan wajen ganin sun jajirce ta fannin neman ‘yancin su.