Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar Da’ira ta tallafawa marasa lafiya a Kano

Published

on

Da’iratul Banatul-Musdafa ta yi kira ga mawadata da su zage damtse wajen taimakawa mabukata musamman a wannan lokaci da ake cikin matsin rayuwa.

Shugabar Da’irar Malama Fiddausi Ishaq Lawal Binta ce ta bayyana hakan lokacin da suke rabon tallafi ga marasa lafiya na asibitin Murtala Muhmammad a yau.

Ta ce, koyarwa ce ta Manzon Allah S.A.W tausayawa mabukaci da mai rauni tare da bashi tallafi a duk lokacin da yake bukatar sa.

Wasu daga cikin marasa lafiya da suka sami tallafin sun bayyanna farin cikin su inda suka ce sun dade suna jinya a asibitin ga yanayin rayuwa do haka sun yi matukar farin ciki da samun sa a wannan lokaci

Wakiliyar Mu Madina Shehu Hausawa ta raawaito cewa Da’irar ta rarrabawa marasa lafiya a bangaren ‘yan karaya da babban daki na mata sabulun wanka dana wanki da omo har ma da sitturu da sauran kayan tallafin jinya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!