Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu fara yiwa fasinjoji feshin maganin corona – NURTW

Published

on

Daga Safara’u Tijjani Adam

 

Kungiyar direbobi ta kasa N U R T W ta ce daga yanzu babu wani fasinja ko direba da zai dinga fita daga garin sa zuwa wani gari ba tare da an yiwa motarsa da kuma fasinjojin motar feshin rigakafin cutar corona ba.

Shugaban kungiyar ta kasa farfesa Tajudden Abinkulle Baruwa ne ya bayyana hakan a yau, a yayin zagayen da kungiyar ta yi a tashar Mariri don raba musu na’urorin feshin maganin da kuma sinadarin wanke hannu.

Farfesa Tajudden ya kara da cewa dukkanin fasinjar da zai fita zuwa wata jihar to dole ne ya kasance yana sanye da takunkumin rufe hanci kuma a tabbatar an yi masa feshin maganin.

Ibrahim Adamu Tiga shine mai baiwa hukumar karota shawara akan tashoshin jihar kano yace yace tuni a jihar kano an dade da rabawa wadannan kungiyoyi takunkumin rufe hanci domin kiyaye kansu, yana mai cewa sun haramta daukan fasinjan kan hanya.

Ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa gwamnatin jihar kano zata samarwa da manyan motocin tireloli tashar da zasu dinga ajiye motocin su domin a daina ganin su a cikin manyan titunan jihar kano

Wakiliyarmu Safara’u Tijjani Adam ta rawaito cewa a yayin zagayen kungiyar N U R T W tayi ta nunuwa mambobinta yadda zasuyi amfani Na’urorin a lokacin daukar fasinjojin da kuma sauke su.

STA/

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!