Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tsaro

Kungiyar dattawan arewa NEF ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da sanyin jiki

Published

on

Mai magana da yawun kungiyar Hakeem Baba-Ahmed ne ya yi wannan zargi a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise, inda ya ce sanyin jikin da Buhari yake nunawa kan sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ya yi yawa.

“Ina mamakin yadda Buhari ya gaza magance matsalolin tsaron Najeriya, kalli yadda sace-sacen mutane ana garkuwa da su sauran ayyukan ‘yan bindiga suka addabi al’umma, wanda a baya can babu wannan matsala” in ji Hakeem Baba-Ahmed.

“Idan na samu damar magana da shugaba Buhari, zan ce ma sa yallabai ka yunkura mana, kasar nan fa tana cikin hatsarin rugujewa a cikin mulkinka, alhalin ka yi rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015 da kuma 2019” a cewar Hakeema Baba-Ahmed.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!