Kaduna
Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a yankin Arewacin Kasar nan

Kungiyar dattawan Arewacin kasar nan, ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta baci a yankin Arewacin Kasar na.
Kungiyar ta gabatar da wannan bukatar ce, sakamakon matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara, wanda ta lalata tattalin arzikin yankin dama kasa baki daya . Mai magana da yawun Kungiyar , Farfesa Abubakar Jiddere ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.
Yace kungiyar ta bayyana damuwarta kan hare-hare da garkuwa da mutane ba kakkautawa da ake cigaba da yi a yankin.
You must be logged in to post a comment Login