Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar dillalan man fetur ta bukaci gwamnati ta biyata hakkinta

Published

on

Kungiyar Dillalan man fetur ta Kasa shiyyar arewacin kasarnan, tayi kira ga gwamnatin tarayya data biya ta bashin wasu kudade sama da biliyan dari biyu da hamsin da mambobin ta ke bin gwamnatin.

Shugaban Kungiyar na kasa shiyyar Arewa Alhaji Musa Yahaya mai kifi ne yayi kiran yayin wani taron gaggawa da suka yi da wasu daga cikin jagororin Kungiyar.

Alhaji Musa Yahaya mai kifi ya kara da cewa ‘kudaden mallakin mambobin Kungiyar ne ba gwamnatin tarayya ba’.

Alhaji Musa Yahaya mai kifi ya kuma ce ‘Kawo yanzu saboda rashin kudin, wasu daga cikin ‘Yan kasuwar basa iya sayan man fetur din duba da halin da kasuwar man ke ciki a wannan lokaci’.

Taron ya samu halartar Sakataren kungiyar Alhaji Zarma Mustapha da kuma shuwagabannin Kungiyar na jahohin dake Arewacin kasarnan.

Rahoton: Ahmad Lawan Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!