Kiwon Lafiya
Kungiyar Gwamnnoni ta mayar da martani kan sashin dake bunciken kudi na kasa
Kungiyar gwamnoni ta kasa ta bayyana cewa sashen binciken kudi na kasa bashi da wata alaka da binciken yadda gwamnonin jihohi ke rarraba kudaden ga kananan hukumomin su.
A wata takarda da kungiyar ta fitar ta hannun kakakin ta Abdulrazak Bello-Barkindo ta bukaci shugaban kasa da ya takawa sashen burki tun kafin lokaci ya kure.
A ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki ne Sahsen na binciken kudade ya fitar da wasu sharruda da ke bayyana cewa ya zama wajibi gwamnonin jihohi su sakarwa kananan hukumomi mara wajen tusarrifi da kudaden su.
Sakamakon hakanne kuma kungiyar ta gwamnoni ta bayyana cewa babu ruwan sashen wajen sanya idanu a kan yadda suke tafiyar da alakar su da kananan hukumomi ta fannin kudi.
Kungiyar ta gwamnoni ta ce sashen na 162 6 cikin baka ya bada dammar samar da asusun bai daya da ya hadar da na gwamnoni da kuma na kananan hukumomi wanda gwamnatin tarayya zata rika biyan su kudin su ta cikin wannan asusun kai tsaye.
Sakamakon hakannen kungiyar ke kiran sashen da ya tsame hannun sa daga shiga cikin ala’amarin.