Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnoni 29 ne suka karbi tallafin kudi a kasar nan – Kayode Fayemi

Published

on

Kungiyar gwamnonin kasar nan tace kimanin jihohi ashirin da tara suka karbi tallafin kudi daga gwamnatin tarayya domin inganta bangaran lafiya a matakin farko wajan gudanar da gwaje gwajan cutar Covid-19.

Kungiyar ta bayyana haka ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a yau alhamis a Abuja wanda shine taro da kungiyar ta gudanar karo na goma sha biyar.

Sanarwa tace gwamnonin da suka hallarci taron sun tattauna abubuwa da suka  damu kasar nan musamman annobar cutar Covid-19.

Bayanai da kungiyar ta karba kan cutar Corona a kasara nan ya nuna cewa kimanain kananan hukumomi ashirin ne a kasar dake dauke da kaso hamsin na wadanda ke dauke da cutar covid-19 a fadin kasar nan.

Sanarwar ta umarci duk gwamnatocin jihohi da su hada kai da kananan hukumomi domin dakile hanyoyin da kaidojin da hukumomin lafiya suka samar wajan kare cigaba da yaduwar cutar ta Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!