Labarai
Kungiyar gwamnoni ta nuna rashin jin dadinta ga zargin su da hana ruwa gudu
Kungiyar gwamnoni ta kasa ta nuna rashin jin dadin ta kan abin da ta kira kalaman karya da ake yadawa a kanta na cewar gwamnonin kasar nan ne suka hana ruwa gudu wajen tabbatar da mafi karancin albashi na naira 30,000
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar Abdulrazaq Bello Barkindo ya fitar da yammacin jiya litini aka rabawa manema labarai.
Ta cikin sanarwar Barkindo ya ce hatta batun naira dubu 22, 500 da gwamnonin suka amince da shi sai da akayi ta tata burza a tsakanin gwamnonin jihohin kasar nan 36 kafin aka cimma matsaya daya.
Ya kuma ce gwamninin sun amince da kudin ne bayan da aka yi nazarin lalitar kowacce jaha da kuma fahin tar cewa hakan shi ne abin jihohin za su iya biya, sannan kuma aka yi la’akari da yanayin tattalin arzikin kasa, da kuma sauran nauyin da ke wuyan gwamnonin tsakanin su da al’umma.
A don haka a cewar sa bai kamata gamayyar kingiyoyin kwadago su zargi gwamnoni da kawo cikas kan batun mafi karancin albashin ba duba da cewar suna nasu kokarin.