Labarai
Kungiyar gwamnoni ta yi alla-wadai da yunkurin hallaka gwamnan Benue
Kungiyar gwamnonin kasar nan ta yi allawadai da harin da ‘yan bindiga suka kai kan jerin gwanon motocin gwamnan jihar Benue Samuel Ortom a jiya asabar.
A jiya asabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jerin gwanon motocin gwamnan a titin da ya hada garuruwan Makurdi da Gboko.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, sanarwar ta yi allawadai da harin da ‘yan bindigar suka kai.
Sanarwar ta kuma nuna alhininta tare da kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye don zakulo wadanda suka kai harin don gurfanar da su gaban kuliya.
Dr Kayode Fayemi, ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce, halin rashin tsaro da kasar nan ke ciki a wannan lokaci, abin damuwa ne saboda haka ya bukaci jami’a tsaro da su kara kaimi wajen kawo karshen matsalar.
You must be logged in to post a comment Login