Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnonin Arewa sun bukaci hadin kan al’umma wajen kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Published

on

Kungiyar gwamnonin Arewacin kasar nan ta bukaci al’ummar Najeriya dake sassa daban-daban a kasar, dama Duniya, da su kara bada hadin kai wajen kawo karshen matsalar tsaro dake addabar Najeriya.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ne ya bayyana hakan a sakon bikin Easter, a madadin kungiyar.

Lalong ya kuma bukaci al’ummar kiristoci da su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaban kasar nan.

Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya kan su ajiye banbancin addini da al’ada da kuma siyasa, tare da tsayawa waje daya domin tabbatar da samnun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!