Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: ‘Yan bindiga sun fasa gidan gyaran hali na garin Owerri tare da sakin daurarru 1500

Published

on

‘Yan bindiga sun kai hari shalkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke garin Owerri tare da cinnawa motoci da ke shalkwatar wuta.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kuma fasa gidan gyarin hali da ke birnin Owerri tare da sakin daurarru dubu daya da da dari biyar.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar wadanda ke da yawan gaske sun tasa keyar jami’an tsaro da ke gadin shalkwatar ‘yan sandan da kuma gidan gyaran halin na Owerri.

Bayanai sun tabatar da cewa ‘yan bindigar sun kona motoci da dama a shalkwatar ‘yan sandan.

A cewar jaridar ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe daya na daren jiya, inda su ka yi ta tabka ta’asa har zuwa karfe uku na asubah.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sai da su ka yi ta rera waka na neman ‘yanci har na tsawon mintuna talatin a shataletalen gidan gwamnati da ke Owerri kafin su kai harin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Imo Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!