Labaran Kano
Kungiyar iyayen yara: ‘ya’ya 47 aka sace mana
Kungiyar iyayen yaran da aka sace a yankin Hotoro da unguwannin da ke kewaye da ita, ta bayyana cewa, tun a shekarar 2016 ne suka fuskanci yawaitar satar yara a unguwannin da suka hadar da Hotoro da Kawo da Walalambe da Tishama da kuma unguwar Walawai inda suka tattara sunayen yara 47.
Sakataren kungiyar Malam Sha’aibu Ibrahim ne, ya bayyana haka n ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan aikin binciko yaran da aka sace a yankunan nasu.
Ya ce sun ruka fuskantar matsaloli tsakanin su da dattawan yankunan da kuma masu unguwanni inda suke karyata rahoton batan yaran, sai dai a wani taro da suka gudanar da masu unguwannin ne suka mika musu cikakken rahoto da sunayen yaran da aka sace din.
Da yake nasa jawabin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa gano yaran da aka yi a garin Onitsha ya biyo bayan matsa bincike da kara fadada aikinsu inda suka je har garin aka kuma samo yaran.
DSP Haruna ya kara da cewa binciken da suka gudanar ya gano ana sayar da yaran ne ga mutanen da ba su samu haihuwa ba.
Da yake yin tsokaci ta cikin shirin, malamin addinin musulunci a nan Kano Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa sakaci aka yin na rashin baiwa shugabannin gargajiya muhimmanci tareda rashin kulawar mahukunta da suka yiwa wadanda za su bada gudunmawa wajen tabbatuwar tsaro.