Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

kungiyar jama’atul nasril Islam ta soki lamarin gwmantin Benue kan rikicin makiyaya da manoma

Published

on

Kungiyar Jama’atul nasril Islam ta soki lamirin gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom da kuma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-kayode kan danganta rikicin Makiyaya da manoma a Jihohin Arwacin kasar nan da cewa ci gaban Jihadin Shehu Usman Danfodiyo ne.

Kungiyar ta JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku da ke da Shelkwata a Kaduna, ta sanar da hakan ne ta-bakin babban Sakatarenta Dokta Abubakar Khalid Aliyu jiya a Kaduna.

Dokta Abubakar Khalid Aliyu ya ce mayar da martanin ya zama wajibi sakamakon sako sunan Mujaddadi Sheikh Usmanu Danfodiyo, wanda ya yi gagarumar sadaukarwa a cikin addinin musulunci da kuma gina al’umma.

Ya kuma ja hankalin al’ummar musulmi su dukufa cikin addu’ar wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar nan, da kuma fatan gudanar da babban zaben kasa na badi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Martanin dai na zuwa ne biyo-bayan wani jawabi da gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya gabatar a wani gidan Talibijin a garin Makurdi da aka yada a sauran kafafen yada labarai dangane da tashin hankalin da ke wakana a Jihar, tsakanin Makiyaya da Manoma.

Yayin da shi kuma Femi Fani-Kayode ya jima yana sukar lamirin al’ummar Arewa ciki har da shugabannin addini.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!