Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar Jama’atul nasril Islam ta bukaci gwamnati tarayya da ta sauke nauyen al’umma

Published

on

Kungiyar Jama’atul Nasril Islam karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Alhaji Sa’ad Abubakar ta ja hankalin gwamnatin tarayya wajen ganin ta sauke nauyin al’ummar kasar nan da ke kanta musamman kare rayuka da dukiyar jama’a.

Babban jami’in yada labaran kungiyar ta JNI Dokta Khalid Abubakar-Aliyu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya bayar jiya Litinin a Kaduna.

Dokta Khalid ya ce kiran ya zama wajibi biyo bayan asarar rayukan jama’a da aka samu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin mutane a karamar hukumar Bassa ta Jihar Plateau a kwanan nan, wanda ya janyo asarar rayuka tare da lalata gidaje sama da 150.

Ya kuma gargadi jami’an tsaro wajen ganin sun yi adalci yayin aikin kwantar da tarzoma a ko ina a fadin kasar nan, sannan ya bukaci hukumomi su dauki matakin hukunta duk wanda aka samu da hannun haddasa rikici a kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!