Kiwon Lafiya
Kungiyar kwadago ta ce ma’aikata sun sha azaba a shekarar da ta gabata
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce shekarar 2018 shekara ce da ma’aikatan kasar nan suka sha tsananin azaba, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen tabbatar da mafi karancin albashi na naira dubu 30.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa kwamared Ayuba Wabba ne ya sanar da hakan lokacin da yake aikewa al’ummar kasar nan sakon sabuwar shekara a jiya Talata.
Ayuba Wabba ya ce duk da nasarar da aka samu da wahalhalun da akasha kafin a cimma matsaya kan batun mafi karancin albashin, amma abin takaicin shi ne har yanzu gwamnatin tarayya ta ki mika kundin gaban majalisun kasar nan domin tabbatar da shi.
Ya kuma zargi gwamnatin da jan kafa kan batun, wanda kuma hakan ke kokarin bata kykyawar alakar da ke tsakanin bangaren gwamnati da kuma kungiyar ta kwadago, da hakan zai iya sanyawa ta sake tsunduma yajin aiki nan da wasu kwanaki masu zuwa
A don hakan ne ya roki gwamnatin tarayyar da tayi abin da ya da ce, wajen tabbatar da cewa an tabbatar da mafi karancin albashin cikin sauri, inba haka ba kuma to shakka babu za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.