Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar kwadago ta ce ma’aikata sun sha azaba a shekarar da ta gabata

Published

on

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce shekarar 2018 shekara ce da ma’aikatan kasar nan suka sha tsananin azaba, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen tabbatar da mafi karancin albashi na naira dubu 30.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa kwamared Ayuba Wabba ne ya sanar da hakan lokacin da yake aikewa al’ummar kasar nan sakon sabuwar shekara a jiya Talata.

Ayuba Wabba ya ce duk da nasarar da aka samu da wahalhalun da akasha kafin a cimma matsaya kan batun mafi karancin albashin, amma abin takaicin shi ne har yanzu gwamnatin  tarayya ta ki mika kundin gaban majalisun kasar nan domin tabbatar da shi.

Ya kuma zargi gwamnatin da jan kafa kan batun, wanda kuma hakan ke kokarin bata kykyawar alakar da ke tsakanin bangaren gwamnati da kuma kungiyar ta kwadago, da hakan zai iya sanyawa ta sake tsunduma yajin aiki nan da wasu kwanaki masu zuwa

A don hakan ne ya roki gwamnatin tarayyar da tayi abin da ya da ce, wajen tabbatar da cewa an tabbatar da mafi karancin albashin cikin sauri, inba haka ba kuma to shakka babu za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!