Connect with us

Kiwon Lafiya

Wasu yan bindiga dadi sun kai hari Dandalin shakatawa a jihar Zamfara

Published

on

A shekaran jiya da daddare ne Wasu ‘yan bindiga suka kai hari dandalin shakatawa a cikin Karamar hukumar Birinin Magaji dake cikin jihar Zamfara,yayin da suka sace mutane 7.

A cewar  mai wurin Shakatawar, Sunusi Iliyasu Ishie ya ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalign karfe 10 na dare, yayin da suka yi garkuwa da mutane 20 a dandalin shakaatawar dake cikin  garin Birnin Gwarin, amma kuma daga bisani suka yi awan gaba da mutum 7 daga cikin su.

Sunusi Iliyasu ya kara da cewar, ‘yan bindigar sun ajiye motocin su nisa da dandalin shakatawar kamar suna gudanar da aikin sintiri daga baya kuma sai suke tambayar nan ne dandalin shakatawar Sunusi? Yace dani da wadandan muke wurin sai muka amsa musu da cewa Eh nan ne, a ganin mu, mun dauka jami’an tsaro ne.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu ya tabatar da afkuwar al’amarin yana mai cewar tuni jami’an ‘yan sanda suka bi byan su, bayan da ta kaddamar da bincike a kan hanyar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,925 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!