Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta tsunduma yajin aiki

Published

on

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a sakamakon rashin biyan mambobinta wasu hakkkokinsu tun daga shekarar 2016 zuwa bana.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Dakta Abubakar Nagoma Usman ne ya bayyana haka, a yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a yau domin shaidawa al’umma halin da ake ciki game da yajin aikin.

Dakta Abubakar Nagoma ya ce akwai kudaden albashi da na alawus-alawus da kungiyar ke bin gwamnati, wanda har yanzu ba su san matsayinsu a kan lamarin ba.

Dakta Abubakar Nagoma ya kuma ce gwamnatin tarayya na korar mambobinta daga aiki, duk da cewa sun sadaukar da rayuwarsu tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19.

Ya kara da cewa kungiyar ta ware wasu wurare domin duba marasa lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!