Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano: Majalisa ta amince da yin gyaran dokar masarautu

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da karatu na biyu na gyaran dokar masarautun jihar, wadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika bukatar hakan.

A kwanakin baya ne dai gwamnan ya aikewa majalisar bukatar yin gyara ga dokar da ta kafa masarautun da nufin kawo wasu sauye-sauye.

Yayin zaman majalisar na yau, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Kabiru Hassan Dashi, ya bukaci goyon bayan ‘yan majalisar kan amincewarsu da karatu na biyu na dokar, inda kuma nan take suka amince.

Kabiru Hassan Dashi wanda kuma shi ne mai wakiltar karamar hukumar Kiru, ya ce, “Yin gyara ga dokar zai sauya tsarin shugabancin sarauta daga rikon shekaru biyu-biyu tare da kara mutum daya cikin masu zabar sarki”.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!