Labarai
Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta yi barazanar tsunduma yajin aiki
Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa (ASUP) ta yi barazanar shiga yajin aiki, matukar gwamnatin tarayya ta kyale hukumar kula da ilimin sana’a ta kasa (NBTE), ta ci gaba da cin zarafin ma’aikatan ta, ta cikin shirin biyan albashin ma’ikata na hadaka.
Haka kuma kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawari kan yarjejeniyar fahimtar juna da suka sanya wa hannu a shekarar da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Usman Dutse.
Sanarwar ta ce kungiyar ba ta zabi da ya wuce ta tsunduma yajin aiki matukar wa’adin kwanaki 21 ya cika ba tare da daukar wani mataki kan lamarin ba.