Labarai
Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta zargi FAAN da karya dokokinta

Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najriya ta zargi Hukumar kula da filayen jiragen sama ta FAAN, da karya dokokin ƙungiyar ma’aikata, tare da neman a ɗauki matakin ladabtarwa kan hukumar.
A cewar shugabannin ƙungiyar, matakan da FAAN ke ɗauka wajen gudanar da al’amuran ma’aikata na sabawa tsarin kundin ƙungiyar, abin da suka ce yana iya haddasa rikice-rikice idan ba a shawo kansa ba.
Sun kuma bukaci hukumomi masu ruwa da tsaki da su saka baki domin tabbatar da cewa an mutunta ka’idodi, tare da kare haƙƙin ma’aikata a bangaren sufurin jirage.
You must be logged in to post a comment Login