Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar MURIC ta ayyana gobe juma’a matsayin ranar makoki

Published

on

Kungiyar da ke rajin kare martabar addinin Islama wato Muslim Rights Concern da akewa lakabi da (MURIC), ta ayyana gobe juma’a, a matsayin ranar zaman makoki don ta ya dalibai musulmi da ke fuskantar cin zarafi a makarantu daban-daban da ke kudu maso yammacin kasar nan alhini, sakamakon dakile musu ‘yancin sanya Hijabi a makaranta.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Farfesa Ishaq Akintola.

 

A cewar kungiyar ta cikin sanarwar, ta dau wannan mataki ne biyo bayan wani faifan bidiyo da ya rika yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka nuno yadda ake cin zarafin wasu dalibai musulmi  a makarantar sakandiren International mallakin jami’ar Ibadan.

 

Sanarwar ta kara da cewa, al’ummar musulmi a duk inda suke a duniya, daya su ke, a don haka kungiyar za ta ci gaba da fafutuka, har sai dalibai mata musulmi sun samu cikakken ‘yanci na zuwa makaranta cikin Hijabi kamar yadda addinin Islama ya umarta.

 

Kungiyar ta MURIC ta cikin sanarwar ta kuma yi kira ga al’ummar musulmi a ko ina suke a fadin kasar nan, da su gudanar da addu’oi domin nemo mafita kan faruwar lamarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!