Kiwon Lafiya
Kungiyar NANS: ta kafa kwamitin na musammam na sarakunan gargajiya da dattawan Najeriya
Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta kafa wani kwamiti na musamman na sarakunan gargajiya da dattawan kasa wadanda za su rika shiga tsakani don sasanta gwamnati da kungiyoyin malaman jami’oi da na kwalejoji.
Shugaban kungiyar dalibai ta kasa Danielson Akpan ya shaidawa manema labarai cewa, sarakunan gargajiya da ke cikin kwamitin sun hada da: Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da kuma Basaraken kasar Ife wato Ooni of Ife Oba Adeyemi Ogunwusi.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce, sauran sarakunan gargajiya da ke cikin kwamitin sun hada da, Obi Of Onitsha, Nnaemeka Achebe da kuma Olowo of Owo Dr Victor Olateru Olagbegi.
Sanarwar kungiyar ta NANS ta kuma ce Chief Edwin Clark da Alhaji Tanko Yakasai da Aare Afe Babalola da Chief Innocent Chukwuma da Mrs. Folorushon Alakija da Farfesa Suleiman Bala Muhammed da kuma Farfesa Rukayya Muhammed.
Haka zalika kungiyar dalibai ta kasar ta kuma nada lauyoyi biyu, Femi Falana da Kayode Ajulo a cikin kwamitin wanda zai rika shiga tsakani tare da bai wa gwamnati shawara da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a gyara bangaren ilimin kasar nan.