Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar NANS: ta kafa kwamitin na musammam na sarakunan gargajiya da dattawan Najeriya

Published

on

Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta kafa wani kwamiti na musamman na sarakunan gargajiya da dattawan kasa wadanda za su rika shiga tsakani don sasanta gwamnati da kungiyoyin malaman jami’oi da na kwalejoji.

 

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa Danielson Akpan ya shaidawa manema labarai cewa, sarakunan gargajiya da ke cikin kwamitin sun hada da: Sarkin Kano  Muhammadu Sanusi na biyu da kuma Basaraken kasar Ife wato Ooni of Ife Oba Adeyemi Ogunwusi.

 

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce, sauran sarakunan gargajiya da ke cikin kwamitin sun hada da, Obi Of Onitsha, Nnaemeka Achebe da kuma Olowo of Owo Dr Victor Olateru Olagbegi.

 

Sanarwar kungiyar ta NANS ta kuma ce Chief Edwin Clark da Alhaji Tanko Yakasai da Aare Afe Babalola da Chief Innocent Chukwuma da Mrs. Folorushon Alakija da Farfesa Suleiman Bala Muhammed da kuma Farfesa Rukayya Muhammed.

 

Haka zalika kungiyar dalibai ta kasar ta kuma nada lauyoyi biyu, Femi Falana da Kayode Ajulo a cikin kwamitin wanda zai rika shiga tsakani tare da bai wa gwamnati shawara da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a gyara bangaren ilimin kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!