Labaran Kano
Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano
Wata Kungiya da ke rajin talafawa marasa karfi mai suna ‘Rumbun Aminci’ ta yi kira ga masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar tallafawa marasa galihu domin samun gwaggwabar lada a gobe kiyama
Shugaban kungiyar kwamared Sani Garba Danjuma ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan gidan rediyo freedom.
Ya ce kungiyar tana ba da tallafin abinci da sutura da kuma kula da harkokin lafiya a wasu daga cikin kananan Hukumomin jihar Kano.
Suna dai samun taimakon kayayyakin sakawa ne daga wajen al’umma, inda suke samun abinci da aka rage daga manyan otel otel sai su alkinta shi yayi daidai da lafiyar abincin da kowa ya ci, sai su rabawa mabukata.
Ya kara da cewa sukan ziyarci makarantun alo da kuma kauyuka don fadakar da su abinci mai gina jiki da ya kamata su dinga ci.
Har ila yau sukan samo abincin mai gina jiki musammam ga yaran da cutar tamowa ya kama su , sukan bada tallafin abincin mai gina jiki da suke samowa don taimaka musu.
A nata bangaren mataimakiyar shugabar kungiyar Malama Hajara Ahmad Rufa’i, ta ce, kungiyar tana mai da hankali ne kan ba da abinci da magungunan da suka shafi zazzabi da ciwon jiki da hawan jini da kuma gyambon ciki.
Dukkanin bakin dai sun kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su rika bai wa marasa galihu fifiko a shirye-shiryen da suke gudanarwa na ci gaban al’umma.