Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Asibitin AKTH zai gudanar da jarabawar kwarewa ga likitoci fiye da dubu

Published

on

Fiye da likitoci dubu daya ne da suka yi karatu a kasashen waje zasu  rubuta jarabawar kwarewa da zai basu damar shiga kungiyar likitoci ta Najeriya a ranar larabar 27 da alhamis 28 da za’a gudanar a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Wanann na kunshe cikin wata sanarwa da sa hannun ofishin sadarwa na asibitin  a jiya wanda yake cewa jarabawar zai baiwa likitocin damar kware tare da basu lasisin gudanar da aikin karkashin kungiyar likitoci.

Ya bayyana cewa shugaban kungiyar da ke lura da jarabawar farfesa Musa Muhammad Borodo ya ce tuni suka gudanar da dukkanin ka’idojin da ya dace domin tafiyar da jarabawar yarda ya kamata.

Sanarwa ta ce an baiwa asibitin damar gudanar da jarabawar tun a shekarar da ta gabata.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!