Connect with us

Labaran Kano

Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano

Published

on

Wata Kungiya da ke rajin talafawa marasa karfi mai suna ‘Rumbun Aminci’ ta yi kira ga masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar tallafawa marasa galihu domin samun gwaggwabar lada a gobe kiyama

Shugaban kungiyar kwamared Sani Garba Danjuma  ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan gidan rediyo freedom.

Ya ce kungiyar tana ba da tallafin abinci da sutura da kuma kula da harkokin lafiya a wasu daga cikin  kananan Hukumomin jihar Kano.

Suna dai samun taimakon kayayyakin sakawa ne daga wajen al’umma, inda suke samun abinci da aka rage daga manyan otel otel sai su alkinta shi yayi daidai da lafiyar abincin da kowa ya ci, sai su rabawa mabukata.

Ya kara da cewa sukan ziyarci makarantun alo da kuma kauyuka don fadakar da su abinci mai gina jiki da ya kamata su dinga ci.

Har ila yau sukan samo abincin mai gina jiki musammam ga yaran da cutar tamowa ya kama su , sukan bada tallafin abincin mai gina jiki da suke samowa don taimaka musu.

A nata bangaren mataimakiyar shugabar kungiyar Malama Hajara Ahmad Rufa’i, ta ce, kungiyar tana mai da hankali ne kan  ba da abinci da magungunan da suka shafi zazzabi da ciwon jiki da hawan jini da kuma gyambon ciki.

Dukkanin bakin dai sun kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su rika bai wa marasa galihu fifiko a shirye-shiryen da suke gudanarwa na ci gaban al’umma.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,987 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!