Labarai
Kungiyar tsoffin Daliban FGC Kano ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan yunkurin yanka filaye

Kungiyar tsofaffin Daliban Makarantar Sakandiren Tarayya ta FGC Kano, ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan abinda ta kira zaluncin da wasu batagari ke shirin yi na yanka filayen makarantar don gina wajen kasuwanci a cikinta.
Mai magana da yawun kungiyar na kasa Kwamred Aminu Haruna Mai Famfo, ne ya bayyana hakan a madadin shugaban kungiyar na kasa Kwamred , Soyinka Soduke, ya yin wani taron manema labarai da ya gudana a harabar Makarantar a yau.
Ya ce ba zasu lamunci halin da aka dauko ba na lalata harkar Ilimi a Makarantar, da Jiha da kasa baki daya.
Kungiyar tsoffin Daliban ta kuma yi kira ga gwamnatin Tarayya da ya dau matakin gaggawa kan Lamarin ta hanyar dakatar da aikin , kana sun gargadi wadan da aka yiwa Tallan siyen filayen makarantar da cewar zasu yi asarar Biyu Babu.
You must be logged in to post a comment Login