Labarai
Kungiyoyin fararen hula a Niger, Mali da Burkina Faso sun yi gangamin kin amincewa da bukatar kasashen Turai

Hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula a kasashen Niger, Mali da Burkina Faso sun gudanar da gangami domin nuna kin amincewa da bukatar kasashen Turai na sakin hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne suka fito kan tituna a wasu manyan birane, inda suka rika daga alluna tare da yin kira ga kasashen waje da su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen yankin Sahel.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa batun tsare Bazoum al’amari ne da ya shafi cikin gidan Nijar kawai, don haka bai kamata kasashen Turai su rika matsa lamba ba kan lamarin.
Haka kuma, kungiyoyin sun jaddada goyon bayansu ga gwamnatocin sojin kasashen uku, suna masu cewa suna kokarin kare ‘yancin kai da mutuncin kasashensu daga abin da suka kira katsalandan na kasashen waje.
Tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2023 ne aka hambarar da Bazoum daga mulki, inda har yanzu yake tsare, duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na a sake shi.
You must be logged in to post a comment Login