Kiwon Lafiya
Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun tsunduma yajin aiki
A yau ne gamayyar kungiyoyin kwadago ta kasa NLC suka fara yajin aikin gargadi sakamakon zargin gwamnatin tarayya da yin kafar Ungulu ga kwamitin tattauna batun mafi karancin albashi.
A jiya Laraba ne dai ministan kwadago da samar da aikin yi Dr Chris Ngige ya yi wata ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago domin samar da mafita kan batun, sai dai an kammala taron baran-baram ba tare da cimma matsaya ba, inda kungiyar ta ce ba gudu ba ja da baya kan yunkurinta na tafiya yajin aikin gargadi farawa daga yau alhamis
Sai dai shugaban kungiyar NLC reshen jihar Kano Kwamared Kabiru Ado Munjibir, ya ce, sun shiga tattaunawa a sakatariyar kungiyar don daukar mataki na gaba.
A jiya Laraba ne dai ministan kwadago da samar da aikin yi Dr Chris Ngige ya ce, za a dawo don ci gaba da tattaunawa kan batun mafi karancin albashin a ranar hudu ga watan gobe na Oktoba.