Labarai
Kungiyoyin masu zazzabar shinkafa 160 suka amfana da tallafi -SAA
Hukumar bunkasa harkokin noma ta Afrika watto sassakawa da kuma shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano KSADP karkashin babban bankin cigaba na Musulunci sun bayyana cewa nan da wasu shekaru jihar Kano zata wadata kasar nan da shinkafa .
Shugaban shirin a nan Kano Abdulrashid Hamisu Kofar mata ne ya bayyana haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai .
Inda yace a shekarar da muke shirin bankwana da ita ta 2023 yace sun taimakawa kungiyoyin manoma shinkafa 160 da kayan zazzabar shinkafa a kanann hukumomi 20 cikin 44 da ake dasu a jihar Kano.
Abdulrashid Hamisu Kofar mata ya cigaba da cewa yin amfani da sabanin dabarun noma wajen noman kayan lambu da suka hada albasa ,Tumatur da kuma Cabeji wata hanya ce da zata samar da kudin shiga a jihar Kano.
Ya kara da cewa hakan ne yasa hukumar taga da cewar ta tallafawa manoma da kayan noman kayan lambu na zamani domin haɓaka noman su a jihar
You must be logged in to post a comment Login