Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kurket: Najeriya ta yi rashin nasara a hannun kasar Kenya

Published

on

Kasar Kenya ta doke Najeriya a wasan Kwallon Kurket (Cricket ), ta kasashe Uku mai taken 4 Tri series dake gudana a kasar Uganda.

Wasan wanda ya gudana Litinin 13 ga Satumbar shekarar 2021, Kasar Kenya ta samu galaba akan Najeriya da gudu 162 ,inda dan wasa Irfan Karim ya samo nasarar gudu 60 da kama Kwallo 45, sai dan wasa Alex Obanda da gudu 33 tare da Rushab Patel da nasarar gudu 26, duk daga kasar ta Kenya.

Kurket: Yan wasan Najeriya sun sauka a kasar Botswana domin wasan share fagen cin kofin Duniya

Daga bangaren Najeriya dan wasa Prosper Useni , ya yi rawar gani inda har ya Samar da makin gudu 17 , da doke sanda sau biyu.

Sai ‘yan wasa Daniel Ajekun mai makin gudu 22 da Joshua Ayannaike da 12 kana Elijah Olalaye da 16, sai Taiwo Muhammad da 21 tare da Mustapha Yusuf mai 12.

Nasarar ta Kenya ta kammala akan Najeriya da gudu 62, Bayan da ‘yan wasan ta Vraj Patel da Peter Koech suka samar Mata da dukan sanda kowanne biyu a cikin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!