Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwalejin Legal ta bada gurbin karatu kyauta ga ƴaƴan marasa ƙarfi

Published

on

Kwalejin addinin Musulunci da harkokin shari’a ta Aminu Kano, ta bayar da guraben tallafin karatu kyauta na mutum 10 ga ɗalibai ƴaƴan marasa karfi da masu buƙata ta musamman da kuma marayu.

Shugaban kwalejin Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ne ya bayyana hakan a yau yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tallafa wa marayu da iyaye mata ta Alkhairi Orphanage and Women Development.

Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ya kuma ce, duk da cewa, zuwa yanzu makarantar ta ɗauki sababbin ɗalibai, amma za su buɗe damar da ɗaliban da ƙungiyar za ta kawo za su ci gajiyar yin karatu kyauta.

“Wannan aiki da Alkhairi Orphanage and Women Development ke yi Sadakatul Jriya be, don haka mu ma bayar da namu tallafin don ganin cewa rayuwar waɗannan yara ta inganta,” cewar Farfesa Balarabe Abubakar Jakada

A jawabinta, babbar Daraktar ƙungiyar ta Alkhairi Orphanage and Women Development Kwamared Ruƙayya Abdulrahman, cewa ta yi sun kai ziyarar ne domin neman haɗin kan kwalejin don sama wa ƴaƴan marasa ƙarfi da na masu buƙata ta musamman da kuma marayu gurbin karatu kamar yadda wasu makarantun jihar nan suka basu irin wannan dama.

Kwamared Ruƙayya Abdulrahman, ta ƙara da cewa i zuwa yanzu ƙungiyar ta samu nasarori da dama musamman a fannin ci gaban ilimi musamman ga ƴaƴa mata.

Haka kuma ta bayyana godiya ga shugaban Kwalejin tare da muƙarrabansa gami da jinjina musu bisa bayar da wannan tallafin karatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!