Labarai
Kwalejin Wasanni ta Jihar Kano Zata Dawo Aiki
Hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, ta ce, tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen ci gaba da gudanar da kwasa-kwasai a kwalejin wasanni ta jihar Kano dake garin Karfi akan titin zuwa Zaria.
Kwalejin dai an samar da ita ne da nufin koyar da masu horaswa tare da ‘yan wasa harma da alkalan wasanni sabbin dabarun aiki tare da basu horo na musamman ta yadda zasu yi gogayya da takwarorinsu na sauran jihohin kasar nan da suka shahara a harkokin wasanni dama duniya baki daya.
Hukumar ta ce kwalejin tana karkashin jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano dake garin Wudil, haka zalika hukumar ta kuma ce tana aiki kafada da kafada da jami’ar don fito da sabbin tsare-tsaren gudanar da ayyuka a kwalejin.
Shugaban Hukumar Alhaji Shariff Rabiu Inuwa Ahlan shine ya bayyana hakan a wata tattauwa da ya yi da wakilin mu Suhaib Auwal Gwagwarwa.
‘‘Yanzu haka an fara shirin hosar da kungiyoyin kwallon kafa guda arba’in da hudu, a yayin da a bangaren masu horaswa aka bukaci kungiyar masu horaswa da ta bada mutane biyu-biyu daga kananan hukumomin jihar Kano, sannan ko wace jiha daga ‘yankin arewa maso yammacin kasar nan suma an nemi su bayar da masu horaswa guda biyu domin fara wannan shirin gagarumin aiki, wanda zai taimaka gaya wajen bunkasa harkokin wasanni a jihar Kano, da Arewa da Nigeria gaba daya’’.
Rashin daukar harkokin wasanni a matsayin sana’a shi ya sanya ‘yan arewa suka zama koma baya a harkokin wasanni
Shariff Ahlan ya kara da cewa bayan kammala daukar horo a wannan kwaleji dalibai zasu karbi shaidar kammala karatu daga jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano dake garin Wudil, inda a cewar sa, hakan zai bawa daliban damar gudanar da harkokin wasanni a ko ina a duniya duba da irin girma da mutunci da wannan jami’a ke da shi a idon duniya.
Shariff Rabiu Inuwa Ahlan wanda kuma shine shugaban kwamitin nada alkalan wasanni a hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni musamman ma ‘yan kasuwa da daidaikun mutane da su shigo don saka hannun jari a fannonin wasanni daban-daban.