Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

RIFAN: ta bayyana matakan da manoma za su karbi bashi

Published

on

Kungiyar manoma shinkafa ta Najeriya RIFAN ta ce an samu nasara sosai a noman shinkafar da aka yi a bana duk da cewa an samu matsaloli a sassan da dama a ayyukan noma.

Shugaban kunigyar reshen jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan Freedom Radio.

Ya ce abinda kungiyar ta RIFAN ta sanya a gaba shi ne ganin gwamnati ta sakarwa manoma shinkafar wadataccen ruwa domin gudanar da noman rani, da za a iya samun amfani mai yawa.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/10/TRACK-UP-HANTSI-RIFAN-HAU-A-07-10-2019.wav-TRACK-UP-HANTSI-RIFAN-HAU-A-07-10-2019.wav-.mp3?_=1

Alhaji Abubakar Haruna ya kuma ce kungiyar na kokari wajen ganin manoman sun samu bashin da zai tallafa musu wajen bunkasa sana’ar su, yana mai cewa gwamnatin tarayya tana bada bashi ga kowanne manomi ba tare da yin zaben wasu ba.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/10/TRACK-UP-HANTSI-RIFAN-HAU-B-07-10-2019.wav-TRACK-UP-HANTSI-RIFAN-HAU-B-07-10-2019.wav-.mp3?_=2

Ya kuma yi bayanin cewa kamata yayi hukuma ta dukufa ainun wajen ganin an samar da wadattun  manoman shinkafa a fadin Najeriya domin ya zamana kasar na iya ciyar da kanta da shinkafar da take samarwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!